Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa Yahya Rasul kakain rundunar sojin kasar Iraki ya bayyana cewa, harin da jiragen yakin Iraki kai jiya a cikin gundumar Anbar sun yi sanadiyyar jikkatar jagoran ‘yan ta’addan Daesh Abubakar Bagdadi, tare da kashe wasu na hannun damarsa.
Jami’an sojin kasar Iraki sun sanar da halaka adadi mai yawa na ‘yan ta’addan IS a yau a garin Mausil na kasar Iraki, da suka hada har da wasu daga cikin manyan kwamandojin kungiyar.
Wasu rahotannin kuma sun ce rundunar sojin kasar ta Iraki ta bayyana hare-haren da jiragenta na yaki suka kaddamar da kan wani dandazon mayakan ‘yan ta’addan IS a cikin Anbar da cewa babbar nasara ce, domin kuwa a cewar bayanin, daga cikin wadanda aka kashe akwai wasu daga cikin manyan na hannun damar Abubakar Bagdadi.
Wasu rahotanni kuma sun ce kotu ta yanke hukuncin kisa kan mutanen da suka tayar da bama-bamai a yankin Bani Sa’ad a cikin gundumar wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, tuni dai jami’an tsaron Iraki suka kame maharan tare da gurfanar da su a gaban kuliya, kuma kotu ta ce za a kashe su ne a bainar jama’a, kuma a daidai wurin da suka tayar da bamai-bamai suka kashe fararen hula.
Sojojin kasar ta Iraki sun bayyana wannan harin da cewa somin tabi ne na ci gaba da kara matsa lamba wajen fatattakar yan ta’adda a duk inda suke acikin fadin kasar ta Iraki, kuma sun kudiri aniyar tsarkake yankunan da ke hannun yan ta’addan.