IQNA

Kungiyar Amnesty International Ta Bukaci A Saki Sheikh Ali Salman

22:48 - November 01, 2015
Lambar Labari: 3431364
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta bukaci hanzarta sakin jagoran ‘yan adawar kasar Bahrain Sheikh Ali Salman.


Kamfanin dilalnicn labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Mir’at Bahrain cewa, kungiyar kare hakkin bil-Adama kasa da kasa, wato Amnesty International ta bukaci da a sakin jagoran ‘yan adawar kasar Bahrain Sheikh Ali Salman ba ta tare da bata lokaci ba.

A bayanin da kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta fitar a jiya Lahadi yana dauke da sanarwar cewa; Mahukuntan gidan sarautar Bahrain suna tsare da Sheikh Ali Salman babban sakataren jam’iyyar Al-Wefaq kuma jagoran ‘yan adawar kasar ne saboda furta albarkacin bakinsa ta hanyar lumana, don haka tana kira ga mahukuntan Bahrain da su hanzarta sakinsa ba tare da gindaya wani sharadi ba.

Har ila yau kungiyar ta Amnesty International ta bukaci gidan sarautar Bahrain da ta mutunta hakkin furta albarkacin baki da duk wani yunkurin ‘yan adawa ta lumana tare da kawo karshen dokokin da suka hana kafa kungiyoyi da jam’iyyun siyasa a kasar.

Tun a ranar ashirin da takwas ga watan Disamban shekarar da ta gabata ta dubu biyu da sha hudu mahukuntan Bahrain suke tsare da Sheikh Ali Salman saboda furta rashin amincewarsa ga munanan matakan da ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ke dauka kan ‘yan adawan Bahrain.

3427105

Abubuwan Da Ya Shafa: bahrain
captcha