Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press TV cewa, Amir Abdullahiyan mataimakin ministan harkokin wajen Iran ya gana da Sayyid hassan nasrullah babban sakataren kungiyar Hizbullah a birnin Beirut.
Tashar talabijin ta Almanar ta bayar da rahoton cewa, bangarorin biyu sun tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi yanking abas ta tsakiya.
Amir Abdullahiyan ya isa kasar ne tare da rakiyar Hamid Reza Dehghan shugaban bangaren kula da harkokin kasashen larabawa da Afirka a ma’aikatar harkokin waje, kamar yadda kuma Muhammad Sadegh Fazli jakadan kasar Iran kasar Lebanon ya tarbe a filin jirgi.
Bayan ganawar dai Abdullahiyan zai gana da wasu fitattun mutane a kasar ta Lebanon da suka hada da shugaban majalisar dokokin kasar Nabeh Berri, inda za su tattauna wasu batu na yankin, musamman ma dai rikicin kasar Syria.
3447417