IQNA

Yahudawan sahyuniya Sun kai Farmaki kan masallacin Quds / Azhar Ta Yi Allawadai

23:18 - December 06, 2015
Lambar Labari: 3460515
Bangaren kasa da kasa, yahudawan sahyuniya sun kai farmaki kan masallacin Quds tare da laada ma masallata duka a cikinsa.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto shafin yaum Sabi cewa, a jiya jami’an tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila sun kame palastinawa sittin da shida a yankin Kalkiliya da ke gabar yamma da kogin Jordan, daga farkon watan ktoban da ya gabata ya zuwa yanzu palastinawa ne suka yi shahada a hannun jami’an tsaron Isra’ila.

Firayi ministan haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi barazaar cewa zai iya rusa masallacin Quds cikin sauki ba tare da wani tayar da jijiyar wuya ba.

Ya yi wannan barazana ne a daidai lokacin da hare-haren yahudawan sahyuniya kan masallacin Quds mai alfarma ke ci gaba da tsananta a cikin lokutan baya-bayan nan, inda yahudawa masu tsatsauran ra’ayi da ke samun kariya daga daruruwan ‘yan sandan Isra’la suke kai farmaki kan masallata a cikin masallacin tare da lakada msuu duka, da kuma harba musu barkonon tsohuwa.

Jami'an Al-azhar ta ja kunnen yahudawan Isra'ila kan kokarin rusa masallancin Al-aqsa

Jami’an alazhar ta kasar masar ta fidda wata sanarwa inda ta yi kashedi wa yahudawan sahyoniyya yan share wuri zauna kan shirinsu na kai hari cikin masallacin al’aksa da kuma rusa shi.



Kamfanin dillancin labaran sana na kasar masar ya naklto jami’ar tana bayyana haka a yau lahadi ta kuma kara da cewa masallacin al-aqsa tana da matukar muhimmanci ga musulmai a cikin Palasdinu da kuma wajensa. Don haka tana kashewa wa dukkan wadanda abin ya shafa da su dakatar da wannan shirin.



3460182

Abubuwan Da Ya Shafa: quds
captcha