Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Abna cewa, sojoji a cikin kayan sarki da motocin Budoza ne suka rusa wurin.
Wadannan sojoji da suke samun umarni daga gwamnatin tarayyar kai tsaye sun dauki wannan mataki ne tun bayan harin da suka kai inda suka yi kisan kiyashi kan mabiya mazhabar shi, inda kuma rusa kabarin mahaifiyar sheikh Zakzaky Hari Jamu.
A baya-bayan nan sojojin an Najeriya sun kai hari kan cibiyar Husainiya inda suka rusata baki daya, kamar yadda kuma daga bisani suka nufi wannan wuri, inda ak arufe mahaifiyarsa da kuma yayansa guda uku da suka rasu a shekarar da ta gabata.
Bayanin ya ci gaba da Hajiya Hari Jamu ta rasu nea cikin watan Muharram na shekarar da ta gabata tana da shekaru 93 a duniya, kuma an rufe ta a garin.
Bayan gudanar da sala ga gawarta a Husainiyar Bakiyatollah wadda danta Sheikh Abdulkadir Yakubu ya jagoranta, kuma dan uwa ga Sheikh Ibrahim Zakzaki, an janazarta a garin an Zaria tare da bizne ta.