IQNA

Mutane 20 Sun Mutu A wani harin Bam A Najeriya

8:29 - January 03, 2016
Lambar Labari: 3480001
Bangaren kasa da kasaAkalla mutane 20 aka tabbatar da cewa sun rasa ransu a wani harin kunan bakin wake a wani kauye jihar Borno a tarayyar Nigeria
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press TV cewa, an kai harin ne a kauyen Jiddari Polo da sanyin safiya a dai dai lokacinda mutanen kauyen suka bada farillan asbaha a ranar Lahadi.
Wani wanda ya ganewa idanunsa ya ce suna cikin sallah ne sai suka ji karar bindiga daga nan kowa ya kama gabansa hatta wadanda suke cikin gidaje suna ta fita suna kama hanyar daji, kuma mutane 91 sun jikkata.
Babakura Kolo wani wanda yake taimakawa jami'an tsaro a cikin harin ya ce mayakan bokoharam sun yi ta barin wuta har zuwa lokacinda sojoji suka fara amfani da makaman attilary.
Wannad shi ne hari na farko a kusa da maidiguri tun tsawon watanni da suka gabata.
3470515
captcha