IQNA

An Kwato Birnin Ramadi Daga ‘Yan Ta’addan Daesh

8:36 - January 03, 2016
Lambar Labari: 3480002
Bnagaren kasa da kasa, rundunar sojin kasar Iraki ta sanar da cewa an kammala aikin kwato birnin Ramadi baki daya daga hannun yan ta’addan Daesh

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ala’alam cewa, rundunar sojin Iraki ta sanar a hukumance a yau cewa, an kammala 'yantar da birnin Ramadi babban birnin lardin Anbar daga hannun 'yan ta'addan Daesh.
Wasu majiyoyin soji a Iraqi sun ce alamu na nuna cewa mayakan kungiyar masu jihadi ta IS sun fice daga ginin da ke dauke da ofisoshin gwamnati a birnin Ramadi.
'Yan kungiyar ta IS dai sun yi garkuwa da wannan gini a lokacin da suke fafatawa da sojojin gwamnati, duk da cewa 'yan kungiyar sun fita daga ginin amma akwai fargabar cewa maiyiwuwa ne sun daddasa bama-bamai kafin su fice.
Sojojin gwamnatin kasar Iraki sun samu gagarumar nasara a kan 'yan ta'addan kungiyar ISIS a garin Ramadi da ke cikin lardin Anbar a yammacin kasar Iraki.

Rahotanni daga kasar Iraki sun tabbatar da cewa dakarun kasar ta Iraki sun halaka adadi mai yawa na 'yan ta'adan, yayin da wasu kuma suka tsere zuwa wasu yankuna da ke karkashin ikonsu.

Gwamnan lardin Anbar ya fadi a daren jiya cewa, 'yan ta'addan sun tafi da wasu daruruwan fararen hula zuwa yankunan Sinjariyyah, da kuma Sufiyyah, inda suka rike su suna masu garkuwa da su.

A wani faifan bidiyo da kungiyar ta fitar, an nuna jagoranta yana bayyana cewa sun yarda sun sha kashi matuka a Syria da Iraki a cikin kwanakin nan, amma duk da haka suna kan bakansu na ci gaba da abin da ya kira jihadi a tafarkin muslunci.

Wasu rahotannin baya-bayan nan na cewa sojojin Iraki sun kafa tutar kasar a farfajiyar ginin da ke dauke da ma'aikatun gwamnati da ke tsakiyar birnin Ramadi, bayan sun fatattaki mayakan kungiyar IS a ranar Lahadi.
Kwace ginin daga ikon kungiyar IS, shi ne abin da sojojin suka dade suna hankoro, mai magana da yawun sojojin Iraki ya ce sunkwato birnin Ramadi.
Kuma jami'an tsaro masu yaki da ta'addanci sun kafa tutar kasar a gine-ginen gwamnati da ke Anbar.
A watan Mayu ne dai kungiyar IS ta kama birnin bayan da ta yi wa sojojin gwamnatin korar kare.
3470470

captcha