IQNA

Saudiyyah ta Amice Da Shiga Tsakanin Muftin Iraki Kan batun Sheikh Nimr

8:40 - January 03, 2016
Lambar Labari: 3480004
Bangaren kasa da kasa, Amir Albayati kakakin ahlu sunna na kasar Iraki ya bayyana cewa Saudiyya ta amince da batun shiga Tsakani na Sheikh Mahdi Sumaidai kan batun Sheikh Nimr
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alfurat News cewa, Amir Albayati kakakin ahlu sunna na kasar Iraki ya bayyana cewa gwamnatin Saudiyya ta amince da shiga Tsakani na Sheikh Mahdi Sumaidai babban mufti na Ahlu Sunnah a Iraki kan hukuncin kisa a kan Sheikh Nimr wanda suka yanke masa.
Ya ce gwamnatin ta Saudiyya ta tababtar musu da cewa ta amince da wannan batu, kuma ministan harkokin wajen kasar ta Saudiyyah Adel Jubair ya tuntubi sheikh Mahdi Sumaidai ta wayar tarho kan batun.
Amir Albayati ya ce daga nan zuwa lokacin da ahlu Sunnah na kasar Iraki za su kammala tattaunawa kan wannan batu, sarkin kasar saudiyya zai bayar da umarni tattaunawa da su kan batun domin sanin abin da za a yi a tsakanin bangarorin biyu.
A kwanakin baya ne dai kotn daukaka kara ta kasar Saudiyya ta tabbatar da hukuncin kisa kan Sheikh Nimr, lamarin da yake fuskantar kakkausar suka daga dukkanin bangarori na duniya.
Akn wannan batu Muhammad Nimr dan uwan sheikh Nimr ya bayyana cewa, an mayar da batun zuwa ga fadar sarkin masarautar al saud domin sa hannu kan zartar da hukuncin kisa kan malamin, amma dai har yanzu ba su uffan kan lamarin ba.
3470682
captcha