Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin
sadarwa na yanar gizo na Alwafd cewam a jiya ne aka gudanar da wani
zaman taro a karkashin cibiyar Azahar domin duba hanyoyin yaki da
tsatsauran ra’ayi tare da halartar malamai.
Jamaluddini Ali Abu Majd
shugaban jami’ar Mina, Mabruk Atiyyah malamin jami’ar Azahar, Sheikh
Hasnain Abdulhakam shugaban bangaren yada addini na ‘aikatar harkokin
addini, sheikh Muhammad sabir shugaban kwamitin fatawa na kasa da dai
sauransu duk suna daga cikin wadanda suka halarci taron.
Mabruk
Atiyyah daga jami’ar Azahar ya bayyana cewa wasu lokuta sakamakon
zalunci a kan al’umma hakan ka iya haifar da tsatsauran ra’ayi wanda zai
iya kai matasa zuwa ga shiga kungiyoyin yan ta’adda.
Ya kara da cewa
hakan zai iya kasancewa ne saboda jahilci da rashin addini a tsakanin
matasa muslmi musamman ma a wannan lokaci da ba su mayar da hankali
wajen bincike kan addini kamar yadda suke kan ilmomi na zamani.
Mabruk
Atiyyah ya kar da cewa a lokacin ma’aiki (SAW) ya kasance shi ne ja
gaba wajen shiryar da al’umma kamar yadda kuma koyarwarsa tana nan sai
ba a aiki da ita, wanda kuma shi ne bababn dalilin fadawar musulmi cikin
yanayin da suka tsinci kansu.
3470307