IQNA

Wani Malamin Yahudawan Isra'ila Na Kira Zuwa Ga Kone Masallatai A Birnin Quds

8:46 - January 03, 2016
Lambar Labari: 3480007
Bangaren kasa da kasa, a ci gaba da nuna banbancin ga musulmi da kiristoci da yahudawan sahyuniya ke wani ya bukaci da akone masallatai da majami’oinsu.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin Palastinu today cewa Wani daya daga cikin fitattun malaman yahudawan Isra'ila ya yi kira ga sauran yahudawa mabiyansa da su fara kona masallatai da majami'oin mabiya addinin kirista da suke cikin birnin.
Shafin ya ce a wata zantawa da malamin yahudawan mai suna Bent Scobchine ya yi da tashar talabijin mallakin gwamnatin yahudawan Isra'ila ta Channel 2 ya bayyana cewa, dole ne su kawo karshen duk wata alama ta wuraren bauta da ba na yahudawa ba a cikin birnin na Quds, da hakan ya hada da masallatan musulmi da kuma majami'oin kirista.
Bayahuden ya ce addinin kirista addinin ne na bautar gumaka, saboda haka ba shi wurin zama a cikin wannan birni.

Wannan dai ba shi ne karon farko da wani malamin yahudawa ya yi irin wannan kira ga sauran yahudawan Isra'ila a kan musulmi da kiristoci dangane da kone wuraren ibadarsu ba.

Babban abin da yafi dagawa musamman mabiya addinin kirsiata mazauan birnin Quds hankali dai shi ne, yadda mutumin ya fito yana yin wannan kira kai tsaye a gidan talabijin na gwamnatin Isra'ila ba tare da wata fagaba ba, kamar yadda kuma babu wani mataki da aka dauka akansa a hukumance.
3471072

captcha