IQNA

Kammala Taron Kasa da kasa Kan tarjamar Manonin Kur’ani A Lebanon

8:57 - January 03, 2016
Lambar Labari: 3480010
Bangaren kasa da kasa, an kammala zaman taro na mai taken tarjama ma’anonin kur’ni mai tsarki a karkashin jagorancin Malek She’ar babban mai bayar da fatawa na Tripoli da ke kasar ta Lebanon a jiya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Altafsir cewa, an gudanar da wannan zaman taro ne bisa gayyatar jami’ar Aljinan da ke birnin, tare da halartar masana da masu bincike daga jami’oi 20 na kasashen duniya.
A lokacin da yake jawabi Zeglol Najjar malami a jami’ar ilmomon muslunci da ke kasar Jordan ya bayyana cewa, tarjama kur’ani mai tsarkia  cikin wasu yaruka na duniya yana da babban tasiri wajen isar da ma’anar kur’ani.
Ya kara da cewa gudanar da wanann bababn aiki tare da bayyana ma’anonin kamlmomin kur’ani da kuma lafuzansa ga sauran al’ummomi na duniya ya zama wajibi a wannan zamani, domin isar da sako ga al’ommomi da harsunansu yana da tasirinsa mai yawa.
Daga karshen taron an fitar da jawabin bayan taro da ke tabbatar da cewa masana da sauran malamai a bangaren lamurra da suka danganci kur’ani daga koina  aduniya dole ne su mike domin isar da sakon kur’ani ga sauran al’ummomi ta hanyoyin da suka dace, an kuma girmama Hashem Alayyubi shugaban jami’ar Jinan.
Kamar yadda kuma bayanin bayan taron ya yi tsokaci kan wasu muhimman lamurran da y ace ya zama wajibi su a mayar da hankali kansu, da hakan ya hada gida cibiyoyin tarjama a kasashen duniya, da kuma samar da hanyoyi na zamani wajen tarjama da watsa ta ga duniya, musamman ma hamyoyin zamani na digital.
3471285
captcha