Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin
sadarwa na yanar gizo na tafsir.ner cewa, wannan gasa an gudanar da ita a
bangaren hardar kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya tare da halartar
mahardata 60 na kasar ta Mauritaniya a birnin Nuwakshot babban birni.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa an bata taken mahir Alkur’ani, wadda ta samu halartar masu gasa su 60 daga fadin kasar.
Cibiyar
gudanar da ayyukan jin kai ta birnin Nuwakshot ce ta dauki nauyin
shirya gasar ta hadar kur’ani baki dayansa, da kuma amsa tambayoyi
daban-daban a bangarori na harda da kuma bayanin ayoyi gami da tajwid.
Alkalan gasa hdu suka jagooranci alkalancinta baki daya har aka kammala , wadanda dukakninsu yan kasar ne.
Daga
karshe a taron girmama wadanda suka nuna kwazo Sayyid Alhaj shugaban
cibiyar ta ayyukan alkhari, da kuma mamba na radiyon kur’ad Sayyid
Muhammad Muhammadu, da kuma mam na kwamitin Fata Uamr Fath Sayyid
Abdulkadir, gami da malamai da masana sun samu halarta.
3471029