IQNA

Kawancen Saudiyyah Na Karfafa Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ne

9:25 - January 03, 2016
Lambar Labari: 3480012
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Jawad Alkhalisi daya daga cikin manyan malaman addini na kasar Iraki ya bayyana kawancen da Saudiyyah ta kafa a matsayin wata hanya ta haifar da ta’addanci da kuma karfafa Isra’ila.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam cewa, Sheikh Jawad Alkhalisi ya bayyana cewa kawancen da Saudiyya ta kafa ban a yaki da yan ta’addan Daesh ba ne, nayaki da hamas da Hizbullah ne da kuma karfafa Isra’ila da sauran bangarori nay an ta’adda a yankin.
Wani abin da ke kara sanya shakku cikin manufar Saudiyya kan kafa wannan hadakar shi ne cewa a daidai lokacin da Saudiyyan take sanar da kafa hadakar fada da ta'addancin, amma gwamnatocin kasashe wadanda suka zamanto tungar 'yan ta'addan a halin yanzu suna zargin kasar Saudiyya.


Tana yin hakan tare da hadin gwiwan kasashe i wadanda su ma suna cikin hadakar, a matsayin kasashen da suke kan gaba wajen goyon bayan ayyukan ta'addancin da ke faruwa a yankin Gabas ta tsakiya musamman a kasashen.

A saboda haka ne da dama daga cikin masana da masu fashin bakin magana suke ganin manufar kafa wannan hadakar karkashin jagorancin Saudiyya ita ce kokarin rarraba kan al'ummar yankin bisa tushen kabilanci da mazhaba.


Haka nan kuma da rufe irin danyen aikin da Saudiyya take yi na kirkirowa da kuma goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin Gabas ta tsakiya da ma sauran yankuna na duniya wadanda a halin yanzu suka fara zama karfen kafa hatta ga kasashen yammaci.
3471283

captcha