Bangaren kasa da kasa, mutanen kasar Bosnia sun tarbi sabuwar shekarar miladiyya ta 2016 da addu'oi da kuma karatun kur'ani mai tsarki, abiranan Sarayevo da kuma Kakani.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na
Arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, mutanen kasar Bosnia wadanda
akasarinsu musulmi ne, sun gudanar da tarukan adduoi da karatun kur'ani
ne domin neman alkharan da ke cikin shekara da kuma neman tsari daga
Allah kan dukkanin sharrukan da ke cikinta.
A yayin adduoin an
gabatar da jawabai na jan hankali da kuma tunatarwa, inda bababn malami
mai baar da fatawa na birnin Sarayevo Anas Liwakovic ya gabatar jawabi
da a cikinsa yake cewa ya zama wajibi a kan musulmi su mayar da hankali
ga addu'oi domin rokon Allah ya kawo bala'oin da suke fuskantar al'ummar
musulmi a wannan duniya, na zalunci da kuma tarwatsa su da rarraba
kawunansu da ake yi.
Daga karshe kuma ya yi jan hankali ga matasan
musulmi da ake yaudararsu ana wanke kwakwalensu ta hanyar cusa musu
muggan akidu na ta'addanci da sunan jihadi, inda sukan zama yan ta'adda
tibran suna masu zaton cewa suna hidima ne ga addinin muslunci, alhali
kuwa musulunci bai koyar da ta'addanci ga mabiyansa, bil hasali ma
musulunci bai yi umarni da a tilasta wani ya yi addini ba.
3471382