IQNA

Mayar Da Martani Kan kisan Ayatollah Nimr

9:34 - January 03, 2016
Lambar Labari: 3480017
Bangaren kasa da kasa, dan uwan Sheikh Nimr da mahukuntan Saudiyya suka kasha a yau ya bukaci mayar da martini ta hanyoyi na lumana.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Shamsu Arab cewa, Muhammad Nimr dam uwan Sheikh Nimr ya bayyana cewa, haki sun girgiza bayan jin labarin cewa an zartar da hukuncin kisa a kansa.
Ya ce ya san cewa dan uwansa mutum ne wanda yake da karbuwa a wajen mutane da dama a duniya, kuma tabbas wannan aiki na masarautar Saudiyya zai fuskanci mayar da martini, amma dai yana bukatar hakan ya zama ta hanyar lumana.
A yau ne ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Saudiya ta sanar da cewa ta hanayar talabijin ta kashe mutane 47 da suka hada da sheikh Nimr.
Mutane 45 daga cikinsu yan kasar Saudiyya ne daya kuma daga Masar, daya kuma daga kasar Chadi.
Wadannan mutane 47 an kasha su a biranan Riyadh, Makka, Madina, Alsharqiyyah, Alkasim, Hail, Asir, Aljauf, Najran, Baha da kuam Tabuk.
3472818
captcha