Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «Politico.com» Hillary Clinton tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka,a lokacin da take amsa tambayoyin manema labarai a jiya ta bayyana kisan da masarautar Saudiya ta yi kan Sheikh Nimr da cewa ba ayi amfani da hikima ba wajen yin hakan.
Ta ci gaba da cewa suna mu’amala da wannan kasa kuma ta san cewa duk abin da za su sukan tuntube su, amma kuma a wannan karo lallai an tafba babban kure kana bin da aka yi.
Ta kara da cewa ta san cewa kowace kasa tana da nata irin dokokin, duk kuwa da cewa dangane da yadda Saudiyya take aiwatar da dokokinta sun hannun riga da mahangar Amurka, amma dai sukan fahimci juna kan batutuwa na siyasa, sai a dai a wannan karon Saudiyya ta aikata wani abu wanda Amurka bata ji dadinsa, domin kuwa kisan fursunan siyasa da sunan aikin ta’addanci abu ne mai muni matuka..