Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa Adel Jubair ministan harkokin wajen kasar Saudiyya a wani taron manema labarai ya sanar da yanke alakar kasarsa da Iran tare da rufe ofisoshin jakadanci a Tejran da Mashhad.
Mataimakin ministan harkokin wajen jamhuriyar Isalama ya bayyana cewa, yanke alaka da Iran da masarautar Saudiyya ta yi, ba zai taba rufe laifin da ta tafka na kashe malamin addini farar hula mai kira zuwa ga adalci da zaman lafiya ba.
Ya bayyana hakan ne a daren jiya a lokacin da
yake amsa tambayoyin manema labarai, inda ya ce tun lokacin da ake gudanar da
tattaunawa kan shirin Iran na nukiliya, masarautar Al Saud ta yi ta kai gwabro
ta kai mari domin ganin tattaunawar ta watse, ta hanyar bayar da cin hanci ga
wasu kasashe da yi musu alkawulla, amma hakan dai hakan bai yi nasara, domin an
cimma yarjejeniyar.
Ya ce baya ga hakan ma kuma masarautar ta Al Saud ta tsaya kai da fata domin
karya farashin kudin amn fetur a kasuwarsa ta duniya domin karya tattalin
arzikin Iran.
Wanda kuma tasirin hakan bai takaita kan Iran
b, ya shafi dukkanin kasashen da suke fitar da danyen man fetur a duniya, wanda
kuma ita kanta kasar da ta kitsa wannan kulli lamarin ya fara shafarta kai
tsaye.
Amir Hussain Abdullahyan ya ce baya ga haka wannan masarauta ta kara kaimi a
cikin yan lokutannan wajen taimaka ma 'yan ta'adda da take yi a yankin, da kuma
kara zafafa hare-hare kan dubban fararen hula da take kashewa a kasar emen.
Baya ga yin sanadiyyar mutuwar dubban alhazai bakin ubangiji da suka tafi safke farali daga dukkanin kasashen musulmi, yanzu kuma ta kashe Sheikh Nimr babban malami a kasar saboda dalilai na siyasa da bangaranci, kuma asakamakon haka ta yanke huldar jakadancinta da Iran, ya ce yanke alaka da Iran ba zai rufe wadannan munanan laifuka da masarautar ta aikata ba.
http://iqna.ir/fa/news/3464437