IQNA

An Dage Gasar Karatun Kur’ani Mai Tsarki Karo 30 A Najeriya

16:23 - January 05, 2016
Lambar Labari: 3480027
Bangaren kasa da kasa, an dage gudanar da gasar karatun kur’anin mai tsarki a karo na talatin Nageriya ba tare da wani karin bayani kan dalilin hakan ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya naalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na AllAfrica cewa, an shirya gudanar da wannan gasa a ne a jahar Nasarawa a ranar 25 ga watan Dei har zuwa 3 ga watan Bahman, amma saboda wasu dalilai an dage ta.

Jami’an da suke kula da shirya wannan gasa dai har yanzu bas u bayyana komai dangane da dalilin da ya sany suka dauki wannan matsaya ba, duk da cewa an saba gudanar da ita akan lokacin da aka ayyana.

A kowace shekara ana gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki a ta kasa baki daya a Najeriya, inda akan zabi wata daya daga cikin jahohin kasar domin gudanar da wannan gasa.

A gasar da ta gabata wadanda suka samu nasara da kuma nuna kwazoa wannan gasa sun samu gurbin karatu a wasu jami’oi na kasashen musulmi kai tsaye.

A cikin mutanen Najeriya miliyan 173, kimanin kashi 55 musulmi ne, kashi 35 kuma kiristoci, 10 kuma masu addinin gargajiya, ko kuma masu bautar dabi’a, daga cikin kashi 55 kimanin mutane miliyan 7 shi’a ne.

3464518

captcha