Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo Knoxnews cewa, wannan taro za a gudanar da shin a tsawon makonni 5 a kowace rana ta Lahadi a majami’ar Protentant a garin Auk Rich na jahar Tency a kasar Amurka.
Bayanin ya ce babbar manufar wannan taro dai ita ce bayar da laccoci da masaniya kan addinin muslunci, kama daga tarihinsa, da bangarorinsa da tarihin annabi Muhammad (SA) da kuma rabe-rabe na sunna da shi’a.
Sharon Yangez daya daga cikin shugabannin majami’oin kasar Amurka, ya bayyana wannan trao da cewa babar dam ace ta sanin addinin muslunci da kuma koyarwarsa ga Amurka mazauna wannan jaha.
A taron wannan babban malamin kirista zai kokari wajen bayyana ma mabiya addinin matsayin mulsunci a tarihi, da wanda mabiyansa suka kai biliyan 1 da miliyan 600 a halin yanzu a duniya, wanda hakan ke nuna cewa sun kai kasha 23% na mutanen duniya baki daya.
Sharman y ace ya jima yana son ya yi Magana kan addinin muslunci tare da wasu, kuma yanzu lkacin hakan ya yi idan aka yi la’akari da halin da ake ciki na nuna kyamar musulunci a kasarsu da kuma duniya musamman a turai, kamar yadda kuma zabuka suke karatowa a kasar, kamfae kan kiyayya da muslunci ya zama a sahun gaba.
Wanann zaman taron dai kofa bude take ga dukaknin Amurka masu bukatar su halarta kyauta, har zuwa lokacin da za a kamala a cikin watan gobe.