Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Pressconnects cewa, Abdulkadir Irere shugaban kungiyar daliban jami’a musulmi ya bayyana rashin amincewarsu da duk wani mataki na hana saka hijabi a kasar.
Irere wanda shi alkalin kotun daukakka kara akotun muslunci da ke cikin jahar Kwara ta Najeriya ya bayyana cewa, babu wani musulmi da zai amince wannan mataki da gwamnatin kasar ke shirin dauka.
Ya ce babu wani dalilai da gwamnati za ta iya fakewa da shi domin hana muusmi mata saka hijabi, domin kuwa yana daya daga cikin lamurra da suke wajibi a cikin addinin muslunci.
Dangane da yadda ake kokarin fakewa da hare-haren da yan Boko haram suke kaiwa akasar kuwa, ya bayyana cewa bababr matsalar da ta haifar da wannan kungiya shi ne rashin ilimin addini a tsakanin matasan kasar.
A kwanakin bayan ne dai shugaba Buhari ya bayyana cewa mai yiwuwa a dauki matakain hana saka hijabi a kasar matukar dai aka ci gaba da kai harin kunar bakin wake.
Kamar yadda kuma bayanin ya kara da cewa, idan aka hana saka hijibi to hakan zai kara kawo rashin tarbiya a cikin al’umma, tare da yin kira da a dauki wasu matakan na daban.
Daga cikin irin matakan da sukeganin ya kamata a dauka kuwa har da matakin yin bincike a wuraren tsayawar motoci da sauransu, da kuma wuraren taruwar jama’a.
http://iqna.ir/fa/news/3466542