IQNA

Gudanar Da Horon Ilmantarwa Kan Musulunci A Zimbabwe

15:44 - January 12, 2016
Lambar Labari: 3480042
Bangaren kasa da kasa, an gudanr da wani taron horar da musulmi domin kara sanin muslunci na kwanaki 20 a Husainiyar Imam Hussaini (AS) a garin Motari na kasar Zimbabwe.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada al’adun muslunci cewa, an gudanar da wani taron horar da musulmi domin kara sanin muslunci, an taron na kwanaki 20 tare da halartar karamin jakadan Iran a kasar, a Husainiyar Imam Hussaini (AS) a garin Motari da ke kasar.

Daga cikin uhimman abubuwan da wannan horo ya mayar da hankali a kansu akwai sanin hakikanin addinin muslunci da koyarwasa, gami da sani tarihinsa da kuma akidojinsa.

Kamar yadda kuma an koyar da ilmin sanin shari’a da hukunci na ibada, da kuma tarihin manzon Allah (SAW) gami da kyawawan dabiu da aka fi sani da akhlaq a ilmance.

Karamin ofishin jakadancin kasar Zimbabwe karkashin jagorancin Shuja Khani ne ya jagoranci gudanar da wannan taron bayar da horo ga mata a kasar, kamar yadda Mehri da Mosavi suka samu halarta, da kuma wasu daga cikin yan shi’a na kasashen ketare da suke zaune a kasar.

http://iqna.ir/fa/news/3466889



Gudanar Da Horon Ilmantarwa Kan Musulunci A ZimbabweGudanar Da Horon Ilmantarwa Kan Musulunci A ZimbabweGudanar Da Horon Ilmantarwa Kan Musulunci A Zimbabwe

captcha