Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin tashar Alalacewa, mutuimin da ya kai harin Istanbul dan asalin kasar Syria haifaffen Saudiyyah ne.
Bayanai daga kasar Turkiyya na cewa an cafke mutun guda da ake zargi da hannu a harin da aka kai jiyya a dandalin sultanahmed na birnin Istambul.
Harin wanda aka kai a safiyar jiyya talata yayi sanadin mutuwar mutane akalla 10 da jikkatar wasu 15 a harin da mahukutan kasar suka dora alhakinsa ga kungiyar 'yan ta'adan daesh ne.
Piraministan Kasar ya bayyana cewa kungiyar ita ce ta kai harin na Istanbul wanda ya salwantarda rayukan mutanen, wanda suka hada da Jamusawa tara.
Ergogan shugaban kasar Turkiya Ya zargi Kungiyar da kai harin ta'addanci a birnin Istanbul.
Ya ce a lokacin ya gabatar da gajeren jawabi ta telbijin ga mutanen kasar ya ce; Bincikenmu ya tababtar da cewa wanda ya kai harin dan kungiyar ce.
Bugu da kari ya ce; "Dukkanin wadanda harin ya rutsa da su, 'yan kasashen waje ne' sannan kuma ya gabatar da ta'aziyya ga iyalansu.
Harin ta'addancin wanda aka kai shi da safiyar yau a tsakiyar birnin Istanbul ya kuma jikkata wasu mutane sha biyar kamar yadda mahukuntan kasar suka bayyana.