IQNA

An Kai Harin Kan Ofishin Kwamitin Taimako Na Imam Khomenei (RA) A Somalia

16:10 - January 13, 2016
Lambar Labari: 3480045
Bangaren kasa da kasa, wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun kaddamar da harri kan babban ofishin kwamitin bayar da agaji na Imam Khomenei (RA) a birnin Magadishou fadar mulkin Somalia.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga wasu shedun gani da ido cewa, wasu mutane dda makamai sun kai hari kan fishin na kwamitin na Imam Khomenei (RA) a birnin magadishou, inda suka kwashe dukkanin dukiyoyin da ke cikinsa baki daya.

Bayanin ya ci gaba da cewa muytane su 5 dukaknins suna dsauke da makamai, kuma sun kai harin ne tare da taimakon wasu mutane ad suke kusa da wurin.

Bayanin y ace an kwashe dukaknin kaddarorin da ke ciki ba tare da gwamnatin Somalia ta iya hana faruwar hakan ba, lamarin da yake sanya shaku kan batun.

Musamman ganin cewa lamari ya faru ne kwanaki 5 kacal da kasar ta sanar da cewa ta yanke alaka da Iran, inda wasu ke ganin cewa aiki ne na ganganci.

Yanzu haka dai jami’an tsaro sun ce suna gudanar da bincike kan lamarin domin daukar matakai da suka dace domin tabbatar da cewa haka ba ta sake faruwa ba.

Jami’an tsaron sun ce sun kame wasu mutane da ake zargin suna da hannu a cikin wannan abin da ya faru.

http://iqna.ir/fa/news/3467266

captcha