
Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga tashar Press TV cewa, wasu masu dauke da makamai sun yi garkuwa da mutane a wani hotel da ke babban birnin kasar Borkina Faso, kuma ya zuwa yanzu an tseratar da mutane 63 daga cikinsu.
Wani jami'in tsaron kasar Borkina Faso, ya sanar da cewa ajiya juma'a da dare ne wasu mutane dauke da makamai su ka kutsa cikin wani babban hotel da ke birnin Ougadugu, sannan su ka yi garkuwa da mutane da dama da ke cikinsa.
Jami'in na 'yan sandar, janderma ya ci gaba da cewa; Mutanen da ake zato masu wuce gona da irin ne, sun kai hari ne akan hotel din Splandid da kuma wata cibiya ta matasa da ke cikin babban birnin.
Tuni dai jami'an tsaron kasar ta Borkina Faso su ka killace wurin, kuma an fara jin karar harbe-harben bindigogi.
Kawo ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani akan ko wadanne irin mutane ne su ka kai wanann harin.
Yanzu haka dai a kasar at Burkina Faso akwai Faransawa da adadinsu ya kai kimanin 3 da 500 da suke raywa a kasar, wasunsu kuma sun zama yan kasa.