IQNA

An Fara Gudanar Da Bincike Dangane Da Kisan Musulmi A Uganda

16:03 - January 18, 2016
Lambar Labari: 3480051
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da bincike dangane da kisan da aka yi wa musulmi 67 a lokacin faduwar mulkin Idi Amin a shekarar 1979.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na World Bulletin cewa, Rohaka Rogonda firayi ministan kasar Uganda, ya bayyana cewa an kafa kwamiti wanda zai fara gudanar da bincike kan kisan musulmi a shekara ta 1979.

A lokacin rikicin da aka yi a kasar wanda ya kai ga faduwar tsohon shugaban kasar a shekara ta 1979, an kashe musulmi kimanin 67 a kasar tare da cin zarafinsu da kuma yi musu barna.

Daga cikina bubuwan da muslmi suka rasa baya ga dukiyoyi da rayuka, har da wuraren ibada, da suka hada da masallatai, da makarantu da kuma cibiyoyinsu na addini.

Wasu daga cikin bata gari da suke jin haushin musulmi a kasar ne suka dauki doka  ahannunsu inda suka yi amfani da dama r da suka samu bayan faduwar shugaban kasar.

Shi dai shugaban kasar a lokacin ya kasance musulmi, duk kwa da cewa ba ya dasawa da turawa, wadanda suka kafa masa karan tsana, daga karshe kuma suka hambarar da shi.

Ksaja Motuno daya daga cikin masu bin bin kadun wannanlamari ya bayyan acewa, a lokacin an yi wa musulmi kisan gila, da ska hada da mata da kanan yara.

A kasar Uganda an yi kokarin ganin cewa an share musulmi baki daya tare da goge sunansu a cikin tsarin mutanen kasar.

3468214

captcha