
Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bernama cewa, gwamnatin yankin Kidah a kasar Mayzia ta bukaci malaman kasar su dauki matakin wayar da kan matasa kan hadarin shiga kungiyar Daesh ta ta’addanci.
Mukhriz Mahatir karamin minister mai kula da yankin ya bayyana cewa, wannan mataki ana bukatarsa a cikin gaggawa, ta hanyar sanar da matasa koyarwar kur’ani kan addini.
Ya ci gaba da cewa sau da yawa ana rudar da matasa ne da sunan addini wajen sanya su su shiga wadannan kungiyoyi ba tare da sun Ankara ba.
Kamar yadda ya ce idan ba a dauki mataki cikin sauri ba, lokacin da za a ankaraabin y agama yin babbar illa a tsakanin matasa musulmi na kasar, wadanda suke da karancin fahimtar addini.
Daga karshe ya ce hakan aiki ne na kowa kama daga kan iyaye da kuma mahukunta da sauran al’umma kasar, da kuma malamai musamman, wadanda su ne suke da ilimi na addini da sanin hanyoyin koyar da shi.