
Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na PressTV cewa, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi kakkausar suka kan kasashen da suke ruruta wutar rikici a yankin gabas ta tsakiya tare da jaddada cewa babu wata riba da zasu samu daga tashe-tashen hankula.
A ganawarsa da manema labarai a gefen zaman taron kasashen hadin kan kasashen musulmi a birnin Jidda na kasar Saudiyya a jiya Alhamis; Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arakche ya bayyana cewa; Wasu kasashe suna kokarin ganin sun kunna wutan rikici da tashe-tashen hankula a yankin gabas ta tsakiya alhalin baba wata riba da hakan zai haifar gare su.
Arakche ya bayyana fatan ganin kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta taka gagarumar rawa a fagen rage kaifin tashe-tashen hankulan da suke ci gaba da addabar kasashen musulmi.
Ya kara da cewa mai makon duba muhimman lamurra da suke da alaka da irin wadannan matsaloli da muslmi suke ciki, kungiyar ta mayar da hankali kan batun farmaki a kan ofishin jakadancin Saudiyya kawai.
Haka nan kuma ya bayyana cewa batun wannan farmaki lamari ne da aka gudanar da bincike kansa har ma da kame wadanda ake zargin suna da hannu, kuma wannan bas hi ne babbar matsalar al’ummar musulmi ba ahalin yanz, matsala ce tsakanin wasu kasashe biyu kawai.
Amma a bin takaici wannan kungiya ta kasashen musulmi ta zama ba ta da damar gudanar da ayyukanta ko daukar matsaya a bisa yanci face abin da wasu suka shirya mata, yace wannan abin takaici kma hakan baya wakiltar dukkanin kasashen musulmi.