IQNA

Indonesia Za Ta Dauki Bakuncin Taron Kasashen Musulmi Kan Quds

23:45 - January 22, 2016
Lambar Labari: 3480067
Bangaren kasa da kasa, kasar Indonesia za ta dauki nauyin bakuncin traon shugabannin kasashen muslmi na gagagwa kan halin da ake ciki a Quds.
Indonesia Za Ta Dauki Bakuncin Taron Kasashen Musulmi Kan Quds
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, bayan da kasar Morocco ta sanar da cewa ba za ta samu damar daukar nauyin bakuncin taron shugabannin kasashen msuulmi kan halin da ake cikia  Quds da Palastinu ba tare da bayyana wani dalili ba, an zabi Indonesia domin gudanar da taron.

Nan da wata daya da wani abu ne za a gudanar da wannan taro, bayan da shugaban Palastinawa Mahmud Abbas ya bukaci hakan, domin tattaunwa da kuma yin dubi kan halin da ake ciki a yankin.

Iyad Amin Madani bababn sakataren kungiyar kasashen musulmin a cikin yan kwanakin da suka gabata ya yi dogwar tattauwa tare da jami’an gwamnatocin Indonesia da kuma na Palastinu kan wannan batu, domin sanin muhimman abubuwan da taron zai tattauna kansu.

Abubuwan da suke wakana a halin yanzu na kisan palastinwa da keta alfarmar masallacin Quds na daga cikin abubuwan da taron zai mayar da hankalia  kansu.

A cikin watan Disamban da ya gabata, birnin Jakarta ya dauki nauyin wani taro mai alaka da batun Palastinu da kuma halin da ake ciki.

3469284

 

captcha