IQNA

Wani Dattijo Yana KOyar Da Kur’ani Kyauta

23:34 - January 23, 2016
Lambar Labari: 3480068
Bangaren kasa da kasa, Amu Ahmad wani dattijo ne da yake koyar da kanan yara karatu da hardar kur’ani mai tsarki kyauta.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Yaum sabi cewa, Amu Ahmad wani dattijo ne dan shekaru 74 da haihuwa kuma maras gani, wanda yake koyar da kanan yara karatu da hardar kur’ani mai tsarki kyauta a kauyen Brim da ke cikin garin Kaum Hamadah a cikin gundumar Buhairah a Masar.

Amu Ahmad an fi saninsa da Ahmad sha’ib a kauyen nasu, kuma yana karantar da yara ne a kauyen karatun kur’ani da harda.

Bisa ga al’ada yara sukan taru a gidansa bayan sallar la’asar, inda yakan fito domin ya karantar da su kur’ani mai tsarki da kuma kaidojin karatun a kowace rana, ba tare da ya nemi lada kan hakan ba.

Da farko dai yak an fara ne da bangaren karatu suna amsawa, daga inda suka kwana, kafin daga bisani kuma ya je bangaren harda domin jin yadda hardarsu take.

Wannan zaman a karantarwa da wannan bawan Allah ke yi dai ya samu karbuwa daga sassa na al’ummar wannan kauye.

3469350

captcha