IQNA

Malamin Kur'ani A Cibiyar Azhar Ya Rasu

23:36 - January 23, 2016
Lambar Labari: 3480069
Bangaren kasa da kasa, Masmu Abu talib fitaccen malamin tafsirin kur'ani mai tsarki ya rasu a jiya bayan fama da rashin lafiya mai tsanani.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na vetogate cewa, masmu Talib malamin tafsirin kur'ani mai tsarki a bangaren ulum Kur'an na jami'ar Azahar ya rasu a jiya bayan fama da rashin lafiya mai tsanani a kasar.

A lokacin sallar Juma a ne a jiya a masallacin Alauda na birnin Jiza aka sanar da rasuwar wannan babban malami wanda ya bayar da gusunmawa.

Bayan da jikin Masmu Abu talib ya yi tsanani saia ka dauke shi wani asibitin soji da ke yankin Alhamimah, inda a can ne Allah ya karbi rayuwarsa.

A yau e dai aka sa ran za agudanar da janar shehin malamin tare da halartar manyan malaman addini da kuma dubban masoyansa daga sassa na kasar ta Masar.

Shi dai wannan malami ya kasance daga cikin manyan malaman sunna wadanda suka bayar da guunmawa ta fuskoki da dama, musamman a bangaren tafsirin kur'ani mai tsarki da kuma ilmomi na kur'ani mai tsarki.

3469345
captcha