IQNA

Za A Gudanar da Gasar Kur’ani Mizamir Dawud A Kasar Algeria

16:55 - January 24, 2016
Lambar Labari: 3480073
Bangaren kasa da kasa, za agudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki mai taken Mizamir Dawud ta yan kasa da shekaru 15 a kasar Algeria.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alhayat cewa, za a gudanar da gasar ta Mizamir ne wadda tashar talabijin ta Al-shuruq TV za ta watsa kai tsaye.

Ridwan Hussain shi ne mai daukar shirin gasar a tashar talabijin ta Alshuruq TV ta kasar Algeria wanda aka gudanarwa akowace shekara mai take Mizamir Dawud, inda yara kan gudanar da hardar kur’ani mai tsarki.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan yana daga cikin shirye-shirye masu kayatarwa da aka saba gudanarwa a waann gidan talabijin tare da halartar malamai makaranta mahardata da suke yin alkalanci a gasar.

Har yanzu dai ba a bayyana lokacin da za a fara gudanar da gasar a wannan shekara ba, amma dai sanarwar ta ce da zaran an kamala dukakanin shirin za a sanar.

Ridwan Hussain mutum da ya shahara akasar wajen mayar da hankali kan yada abubuwa da suka shafi kur’ani da koyrwarsa ta hanyoyi na yada labarai da sauran kafofin sadarwa na zamani, inda ake yi masa lakabi da mai hidimar Haramain.

Daga cikin shirinsa akwai shirin karantun littafin Zabur, wanda aka rubuta a cikin harshen larabaci da yake bayani kan wa’azi da kuma fadakarwa ga al’ummar musulmi na kasar, wadanda suke cikin bukatar fadakarwa.

3469585

captcha