
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na "cairoportal.com” cewa, Shauki Allam babban mai bayar da fatawa a kasar Masar a yayyin taron tattaln arziki na birnin Davos ya ya gana da John Kerry sakataren harkokin wajen kasar Amurka.
Shauki Allam ya bayyana a yayin ganawarsu cewa, samuwar musulmi a cikin kasar Amurka abu ne mai kyau, domin kuwa nuna cewa addininsu na ‘yan adamtaka ne.
Ya kara da cewa mabiya addinin mulsuncia duk inda suke da hakan ya hada da kasar Amurka, suna a matsayin masu wakiltar addininsu ne, ta hanyar nuna kyawawan dabiu a cikin dukkanin rayuwarsu.
Kamar yadda kuma ya yi ishara da cewa, a kowane lokaci musulmi suka fuskanci matsala sakamakon abin da wasu wawaye suke aikatawa da sunan muslunci, sai hakan ya kara ba su damar bayyana wa duniya cewa addininsu na zaman lafiya ta fahimtar juna.
Haka nan kuma ya bayyana cewa ya ji dadin ganawarsa da sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka, domin kuwa acewarsa hakan wata dama domin bayyana muhimman lamurra da ya kamata a kara fahimta dangane da muuslmi mazauna kasar da kuma yadda ya kamata a kara kare hakkokinsu.
Zaman taron dai ana gudanar da shi kan harkokin tattalin arziki na duniya, tare da halartar shugabanni da jami’an gwamnatoci daga kasha 150 na duniya, inda ake bayyana ra’ayi da mahanga kan lamurra da dama da suka shafi duniyar yau.