
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga
shafin sadarwa na yanar gizo na Almasa cewa, bisa yarjejeniyar da aka
cimmawa atsakanin ma’aikatar kula da
harkokin addini a lardin Masila, masan kan harshen ishara za su rika nuna wa
kurame abubuwan da ake fada ahudubar
juma’a.
An sanya hannu kan wannan yarjejeniya ne tare da halartar Muhammad Isa minister mai kula da harkokin ddini a kasar ta Algeriya a masallacin Ali bin Abi Talib (AS) da ke Masila.
Bisa ga wannan yarjejeniya, masana kan harshen ishara za su rika yin bayani a lokacin hudubar juma’a, kamar yadda kuma za su rika koyar da kurame ilmomin addini.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shiri za a fara aiwatar da shi daga wannan gunduma, inda kuma ake sa ran zai samu karbuwa daga sauran al’ummomin gundumomin kasar.
Nan ba da jimawa ba ne za a fara aiwatar da shirina dukkanin masallatan juma’a na gundumar masila, inda kuma shirin hada har da cibiyoyi na addini, musamman dai makarantu da ake koyar da dalibai.
Ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Algeriya ta ce it ace da kanta za ta dauki nauyin shirin da kuma gudanar da shi a wannan gunduma a matsayin matakin farko, kafin daga bisani a ci gaba da fadada shi.