
Kamfanin
dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar
gizo cewa, ministocin kula da harkokin addini na kasashen musulmi a taron da suke
gudanarwa kan yaki da tsatsauran ra’ayi a tsakanin mabiya addinin muslunci a
kasar Morocco sun jaddada wajabcin shiga kafar wando da akidar nan ta
tsatsauran ra’ayi da ke kai muslmi zuwa ga ta’addanci.
Ahmad Taufiq
minister mai kula da harkokin addini a kasar Morocco ya bayyana a lokacin bude
taron cewa, ya zama wajibi a kan dukaknin kasashen musulmi su dauki matakan da
suka dace domin magance wannan matsala.
Shi ma a
nasa bangaren Ahmd Juma’a tsohon mai bayar da fatawa na kasar Masar ya bayyana
cewa, ya kamata majalisar dinkin duniya ta hada kai da kasashen domin fuskantar
wannan lamari wanda yak e ciwa kowa tuwo a kwarya.
Shi ma
Muhammad Yusuf ministan harkokin addini na kasar Pakistan ya jaddada cewa
kasarsa ba za ta kasa a gwaiwa wajen ci gaba da fuskantar wannan lamari ba.
Baba Sisi
ministan addini na Senegal ya irayi dukkanin kasashe da su bayar da hadin kai
wajen ganin an yai tsatsauran ra’ayi, domin kacewa faruwar ayyukan ta’addanci
da ke barazana ga kowa.
Abdullah Bin
Bih shugaban kungiyar yada lamurran addaini a kasar UAE ya bayyana cewa, wannan
aiki ya rataya adukkanin kasashen duniya
duniya, a kan haka a shirye suke s yi aiki da dukkanin kasashe domin tabbatar
da wannan manufa.
Malamai 150
da kuma ministocin addini 40 daga kasashen duniya 100 ne suke halartar zaman
taron, wanda yake samun halartar was bangarorin majalisar dinkin duniya da kuma
kngiyoyi na kasa da kasa, wanda ake gdanarwa a kasar ta Morocco yanzu haka.