IQNA

Kashi 80 Na ‘Yan Ta’addan Daesh A Libya ‘Yan kasashen Ketare Ne

22:36 - January 27, 2016
Lambar Labari: 3480084
Bangaren kasa da kasa, jakadan Iran a kasar Libya ya bayyana cewa kimanin kasha 80 cikin dari nay an ta’addan Daesh da ke yakia Libya yan kasashen ketare ne.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na Sporting News cewa, Hussain Akbari jakadan Iran a kasar Libya cewa kimanin kashi 80 cikin dari na yan ta’addan Daesh da ke yakia  Libya yan kasashen waje ne da ska shigo ksar, amma kadan ne daga cikinsu yan asalin kasar.

Akbari ya ci gaba da cewa, da dama daga cikinmutanen Libya suna goyon bayan juyin juya halin da aka yi a kasar, amma bas u goyon bayan abin da yake faruwa  ahalin yanzu, inda yan ta’adda na kasashen ketare suka mamaye komai a kasar.

‘yan ta’addan Daesh suna da sabani da dukaknin bangarorin masu dauke da makamai a kasar Libya, da hakan ya hada da wadanda suke rike da wasu yankuna  ayammaci da gabashin kasar, wanda hakan ya sanya suke da ta bata kashi a tsakaninsu.

Hussain Akbari ya kara da cewa, kungiyar Alkaida tafi karfi a cikin kasar ta Libya, saboda su yan kasar ne sun kan lagonta, amma Daesh suna shigo da mayaka daga kasashen ketare ne.

Ya ci gaba da cewa babban burin yan ta’addan daesh shi ne su mamaye wurare da suke da arzikin danyen man fetur, kamar yadda yanzu haka wasu yankunan ke a karkashin ikonsu, bayna da suka kori dakarun gwamnati.

Jakadan na Iran ya ce babbar hanyar kawo karshen wannan rikici ita ce bayar da damar zaunar da bangarorin da ke dake da makamai kan tebur da kuma sanya su ajiye makamai.


 3470874 

captcha