
Kamfanin dillancin labaran iqna ya
habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na PressTV cewa,
akalla mutane 5 ne daga cikin jami’an yan sandan kasar suka rasa rayukansu.
Joseph Bonet babban jami’in yan
sanda na Kenya ya tabbatar da wannan bayani na kisan jami’an yan sandan kasar.
Tun kafin wannan lokacin dai kungiyar
ta Alshabab ta sha alwashin kai munanan hare-hare a cikin kasar ta Kenya.
Wasu daga cikin wadanda suka shida
abinda ya faru sun bayyana cewa an kai harin ne a lokacin da jami’an yansanda
10 ne a wurin.
Wannan harin yazo bayan wani
makamancin sa da yan ta’addan na shabab suka kai yamma maso kudancin kasar a
kwanakin baya, inda suka kashe mutane 8 daga cikin jami’an tsaro.
A cikin lokutannan dai mayakan na
shabab sun tsananta harinsu kan jami’an tsaron Kenya, babu kakkautawa.
A cikin makonni biyu da suka gabata
ma sun ce sun kashe sojojin Kenya awani
sansani na dakarun majalisar dinkin duniya a cikin kasar Somalia, amma har
yanzu Kenya ba ta ce komai kan batun ba.