
Kamfanin dillancin labaran iqna ya
habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na mujaz Irak cewa,
babbar cibiyar kula da ayyukan mabiya mazhabar shi’a aIraki ta sanar da cewa Azahar ta janye gasar
da ta shirya kan kalubalantar shi’a a cikin mabiya tafarkin Sunnah.
Matakin janye gudanar da wannan gasa
ya zo ne bayan ganawa Tsakanin Ahmad Tayyib da kuma jakadan kasar Iraki a
Masar.
Azahar ta bayyana cewa ta dauki
wannan matakin ne saboda tana son hadin kai a tsakanin dukkanin al’ummar
musulmi, kuma duk abin da zai kawo rarraba tsakanin musulmi ya kamata a kauce
masa.
Tun a kwanakin baya ne cibiyar ta
sanar da wata gasa mai take hadarin yadwar shi’a a ttsakanin yan ahlu sunna, da
kuma hanyoyin da za a bi domin hana ci gaban hakan.
Kamar yadda kuma ta sanar da cewa za
ta bayar da kyauta ta kudi lakadan ga duk wadanda suka shiga gasar da kuma
wadanda suka nuna kwazo musamman.