IQNA

Mauritaniya Ta Janye Batun Rufe Wasu Makarantun Kur’ani

23:27 - January 29, 2016
Lambar Labari: 3480089
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Mauritaniya ta janye da batun rufe wasu daga cikin makarantun kur’ani mai tsarki a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na islamtoday.net cewa, gwamnatin kasar Mauritaniya ba tare da wani Karin bayani ba, ta janye da batun rufe wasu daga cikin makarantun kur’ani mai tsarki a lardunan Haud Sharqi da Haud Garbi.

Bayanin da mahukuntan kasar suka bayar ya bayyana cewa makarantun da aka dakatar za su iya ci gaba da gudanar da harkokinsu na karatu kamar yadda suka saba  alokutan baya.

Tun kimanin watanni biyu da suka gabata ne dai mahukunatn kasar Mauritaniya suka sanar da cewa saboda yin amfani da ake da makarantun kur’ani wajen yada tsatsauran ra’ayi sun rufe wasu makarantu.

Sheikh Muhammad Alhassan Aldud shugaban babbar cibiyar harkokin addinin muslunci ta kasar Mauritaniya ya bayyana cewa wannan mataki bai dace ba, kuma ya yi kakakusar suka kan hakan, tare da kiran mahukuntan kasar da su canja shawara ba tare da bata lokaci ba.

Y ace makarantun kur’ani mai tsarki su ne izza da daukakakr kasar Mauritaniya, kuma rufe su bababn kurta ne wanda baya da wani abin da zai wanke hukuma a kansa, a kan haka suna bukatar a janye wannan mataki cikin gagagwa.

3471051

captcha