IQNA

An Bukaci Kare Hakkokin Mabiya Addinai Marassa Rinjaye

23:32 - January 29, 2016
Lambar Labari: 3480090
Bangaren kasa da kasa, an bukaci da a kiyaye hakkokin mabiya addinai marassa rinjaye a taron da aka gudanar a kasar Morocco kan kare mabiya addinai marassa rinjaye a kasashen musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alhurrah cewa, a jiya an bukaci da a kiyaye hakkokin mabiya addinai marassa rinjaye a taron da aka gudanar a kasar Morocco kan kare mabiya addinai marassa rinjaye a kasashen musulmi da suke rayuwa a cikinsu.

Wannan taro ne an gudanar da shi a mataki na kasa da kasa, tare da halartar mutane fiye da 300 da ska hada da malamai da masana da kuma ministocin kula da harkokin addini na kasashen musulmi fiye da arbain, wanda suka tattauna kan yadda za a kare hakkokin mabiya addinai mazauna kasashen muslmi.

Kafofin yada labarai da dama a kasar ta Morocco sun bukaci mahalarta taron da sukafitar da matasa guda daya, dangane da yadda ya kamata kasashen msulmi su dauki matakan da suka dace wajen kare rayukan wadanda ba musulmi ba a kasashensu, tare da wayar da kan masu tsatsauran ra’ayi kan cewa wannan ba maslaha ce ta addinin muslunci ba.

A nasu bangare mahalrta taron sun mika nasu sakonni ga gawmnatoci na kasashen msuulmi domin daukar wannan mataki na kare mabiya addinai marassa rinjaye a cikin kasashenu, kamar yadda kuma ska bukaci sauran kasashe wadanda musulmi ba da su ma su kare rayukan musulmi a cikin kasashensu.

3471070

captcha