
Kamfanin
dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar
gizo na shin huwa cewa, a harin da aka kai kan masallacin Imam Rida (AS) a
yankin Ihsa da ke gabacin Saudiyya mutane 4 sun rasu, wasu kimanin 18 sun
jikkata.
A
nasa bangaren kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya nuna damuwa kan abin
da ya faru na kai wannan harin ta’addanci kamar dai yadda bayanin ya ce.
Kwamitin
tsaron yay i kira ga kasashen duniya kan su taimaka ma gwamnatin Saudiyya wajen
fuskantar wanann matasala.
Kamar
yadda kuma ya bayyana hakan a matsayin aikin dabbanci da kisan gilla kan bil
adama ba tare da rahma ba.
Cibiyar
Azahar ita ma ta fitar da nata bayanin da ke cewa wannan ikin na barna, wanda
ake kaiwa kan wuraren ibada, tare da keta alfarmarsu, wanda hakan ya yi hannun
riga da koyarwar muslunci.
Wannan
dai ba shi ne karo da aka kaddamar da harin ta’addanci kan mabiya mazhabar
shi’a ayankin ba.