IQNA

Ana Shirin Samar da Tsarin Kudi Na Muslunci A Kasar Kenya

21:39 - January 30, 2016
Lambar Labari: 3480093
Bangaren kasa da kasa, an a shirin samar da wani tsari na kudade a kasar Kenya bisa tsarin kudi irin na addinin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anatoli cewa, ana shirin gudanar da tsarin kudi irin na musluuncia  kasar Kenya duk kuwa da cewa akasarin mutanen kasar mabiya addinin kirista.

Amma duk da haka gwamnatin kasar ta zabi ta yi aiki da wannan tsari saboda gamsuwa da shi.

Henry Rotich wanda shi ne ministan kudi na kasar ta Kenya ya bayyana cewa wannan shi ne karon farko da ake gudanar da irin wanann tsaria  wata kasa daga cikin kasashen nahiyar Afirka, wanda kuma ko shakka babu zai taimaka matuka wajen gudanar da lamurra da dama ta fuskar kudi a kasar ba tare da matsala ba.

Ya kara da cewa tun shekarun da suka gabata ne aka fara shirin aiawatar da wannan tsari, bayan da masana harkokin tatalin arziki suka amince da shia  kasar.

Haka nan kuma a cewarsa kasashen mambobi a kungiyar kasashen musulmi za su iya amfana da hanyoyin saka hannyaen jari bisa wannan tsari a kasar, ta hanyar yin mu’amala da kasar bisa cinikiyya da harkokin kudi a muslunce.

3471225

captcha