
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin jagora cewa, jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ba wa kwamandojin sojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran su biyar da suka jagorancin kame sojojin ruwan Amurka da suka shigo ruwan kasar Iran a kwanakin baya lambar girma ta "fath' (nasara) don jinjinawa wannan namijin kokari da suka yi na kare kasarsu.
A yau Lahadi ne Ayatullah Khamenei ya ba wa Rear Admiral Ali Fadavi.
Kwamandan sojin ruwa na dakarun kare juyin juyin juya halin Musulunci da wasu manyan kwamandojin dakarun kare juyin su hudu lambar girman soji na "Fath" saboda kokarin da suka yi wajen jagorantar sauran dakarun kare juyin da suka kame sojojin Amurkan da suka shigo cikin ruwan Iran a kwanakin baya ba tare da izini ba.
A makon da ya wuce ma dai Jagoran juyin juya halin Musuluncin, a wata ganawa da yayi da kwamandoji da sauran dakarun kare juyin da suka kame sojojin Amurka, ya jinjinawa wa wannan aiki da suka yi wanda ya bayyana shi a matsayin jaruntaka kana kuma aikin da aka yi a daidai lokacin da ya dace.
Idan dai ana iya tunawa a ranar sha uku ga watan Janairun nan da muke ciki ne, dakarun kare juyin juya halin Musuluncin suka sanar da kame wasu sojojin Amurka su 10 da suka shigo cikin ruwan kasar Iran ba tare da izini ba, sai dai daga baya an sake su lokacin da ya bayyana cewa sun shigo cikin gidan Iran din ne bisa kuskure, sannan kuma gwamnatin Amurka ta gabatar da neman afuwarta da wannan kuskuren da sojojin nata suka yi.