
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Misral Yaum cewa, Muhammad Mukhtar Juma’a ministan harkokin addini Masar ya jagoranci bude cibiyar ta hardar kur’ani mai ta hanyar zamani a lardin Bahrul Ahmar.
Istan mai kula da harkokin addinai a kasar ta Masar ya jagoranci bikin bude wannan babbar cibiyar wadda za ta rika kula da harkokin hardar kur’ani mai tsarki a lardin, wanda zai zama karon farko, kafin daga bisani a fadada shirin.
A lokacin yake ganawa da malamai masu kula da wadannan ayyuka da za su kasance masu bayar da horo a wannan cibiya, ministan ya jadda muhimmancin mayar da hankali wajen kula hardar yara musaman ma, wadanda su ne manyan gobe kamar yadda ya bayyana su.