
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga SANA cewa, , Wa’il Halaki firayi ministan kasar Syria a wani bayani da ya fitar ya bayyana harin da aka kai yau a yankin Zainabiyya na birnin Damascus da cewa masu daukar nauyin yan ta’adda suna yunkurin karfafa su ne.
Rahotanni daga kasar Siriya sun bayyana cewar alal akalla mutane 45 sun rasa rayukansu kana wasu da dama kuma sun sami raunuka sakamakon wasu hare haren ta'addanci da aka kai yankin Sayyida Zainab (a.s) da ke bayan birnin Damascus, babban birnin kasar Siriyan.
A wata sanarwa da ma'aikatar cikin gidan kasar Siriya ta fitar, ta bayyana cewar alal akalla mutane 60 sun rasa rayukansu kana wasu fiye da dari kuma sun sami raunuka sakamakon fashewar wata mota da aka makare ta da abubuwan fashewa a wani yanki da ke kusa da Hubbaren Sayyida Zainab, jikar Manzon Allah (s) da ke yankin na Zainabiyya. Har ila yau bayan fashewar motar kuma wani dan ta'adda da shi ma yayi jigida da ababen fashewar ya tada kansa lamarin da yayi sanadiyyar mutuwa da kuma raunana wannan adadi na mutanen.
Tuni dai kungiyar ta'addancin nan ta da'esh ta sanar da daukan alhakin kai wadannan hare-hare na ta'addanci.
Shekara da shekaru kenan dai 'yan ta'addan suke son kama wannan yankin amma tsayin dakan sojojin Siriya da dakarun sa kai na kasar da kuma na dakarun kungiyar gwagwarmaya abanon sun hana su cimma wannan manufa ta su.