IQNA

Koyar Da Karatun Kur’ani Ga Wadanda Ba Larabawa Ba A Amurka

22:15 - February 01, 2016
Lambar Labari: 3480100
Bangaren kasa da kasa, an samar da wani shiri na koyar da Amurkawa musulmi wadanda ba larabawa ba karatun kur’ani mai tsarki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Saudiyya Today cewa, wannan shirin zai hada Amurkawa wadanda ba larabawa da suke bukatar koyon karaton kur’ani mai tsarki.

Rashad Hassan daya da cikin wadanda suka kirkiro wannan shiri ya bayyana cewa, babbar manufar hakan ita ce tabbatar da cewa mutanen da bas u fahimtar harshen larabaci wadanda kuma muuslmi ne  akasar ta Amurka ba a haramta musu koyon karatun kur’ani ba.

Bayanin ya ci gaba kafin wannan lokacin an samar da wasu shirye-shiryen na koyar da Amurkawqa karatun kur’ani mai tsarki, amma a wannan karon shirin zai banbanta da sauaran wadanda aka gudanar.

Domin a lokutan baya an yi afani da yayi koyarwa ne wanda aka saba a sauran wurare, amma a yanzu za a yi amfani da sabuwar fasaha ta zamani domin aiwatar da shirin.

Musulmi da dama ne dai suke zaune a kasar Amurka, wadanda akasarinsu kuma ba yan asalin kasar ba ne, wasu daga cikinsu larabawa ne, wasu kuma yan kasashe daban-daban.

Yanzu haka dai wannan shiri ana gab da fara aiwaar da shi kamar dai yadda aka shirya, tare da taimakon wasu daga cikin cibiyoyin musulmi na kasar.

3471817

captcha