
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na The Art Newspaper cewa, an shiya gudanar da wani abbabn baje kolin kur’ani a wata cibiya al’adu a cikin watan Oktoba wanda za a gudanar da zaben shugaban Amurka.
Bayanin y ace wanann baje yana da matukar muhimamnci, domin kuwa a cikinsa za a baje kolin wasu daga cikin daddun kwafin kur’ani mai tsarki daga kasashe masu tarihi na yankin gabas ta tsakiya, na larabawa da farisawa da turkawa da sauransu.
Babbar cibiyar bincike kan harkokin al’adu ta birnin ta dauki nauyin gudanar da wanann baje koli, wanda kuma ake sa ran zai samu halartar Amurkawa da dama, musulmi da ma wadanda ba musulmi ba mazauna birnin.
Daga cikin kwafin kur’ani da ke wurin, akwai wanda an rubuta his tun kimanin shekaru 900 da suka gabatana ajiye da shi a wani dakin ajiye kayan tarihi na birnin Damascusn akwai kuma wadanda aka rbuta tun lokacin Usman, an kuma fitar da su a cikin karni na 16, da 17.
Baya ga haka kuma za a nu wasu daga cikin kayan tarihi da suke da alaka da addinin muslunci a wannan baje koli.
Ma’asuma Farhad daya daga cikin wadanda suka shirya wannan baje koli ta bayyana cewa, babbar manufar sui ta ce kara fito da matsayin addinin muslunci da tarihinsa da kuma abubuwan da yake da su masu kima a tarihinsa.