
Kamfanin
dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Dini Haber cewa,
Mariya yar shekaru 7 ce yanzu da take rayuwa a yankin Lotin da ke arewacin
birnin London.
Mahaifiyarta
dai ta bayyana cewa Mariya ta hardace surat Yasin tun tana shekaru 5 da
haihuwa, daga nan kuma ta ci gaba da hardar kur’ani mai tsarki.
Ta
kara da cewa babban abin da y aba su mamaki shi ne yadda wannan yarinya take da
saurin fahimta da kuima rike abin da aka gaya mat aba tare da mantawa ba.
Mahaifiyar
ta ce ta sanya diyarta makarantar addini domin koyon karatun kur’ani, amma idan
ta dawo gida tana koyar da ita musamman.
Mariya
ta kan zauna tare da mahaifiyar tsawon sa’oi 5 tana koyon karatun kur’ani da
harda tare da mahaifiyar a kowace rana.
Mahaifiyarta
ta zama bababn abin buga misali da ita
atsakanin mata musulmi da suke bayar da muhimmanci matuka ga lamarin kur’ani
tare da koyar da yaransu.