IQNA

An Gudanar Da Janazar Ragib Mustafa Galwash A Mahaifarsa

21:00 - February 05, 2016
Lambar Labari: 3480111
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da janazar fitattace makarancin kur’ani Ragib Mustafa Galwash a kauyen Barma da ke garin Tanta a gundumar Garbiyyah.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Albawwabah News cewa, dubban mutanen ne suka halarci janazar marigari Galwash a kauyensu na Brma inda aka rufe shi a jiya.

Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da sallar mamaci a kan gawar Ragib Mustafa Galwash a wani masallaci da aka sakawa sunansa a kauyen nasu na Barma, inda dubban masoyansa da suka hada da yan uwa da abokan arziki da jama’ar gari suka taru a wajen wannan janaza.

Ragib Mustafa Galwash ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya na tsawon lokaci, inda ya rasu a ranar laraba da ta gabata awani asibiti yana da shekaru 77 a duniya.

Ragib Mustafa Galwash an haife shi ne a cikin shekara ta 1939 a kauyen Barma a cikin gundumar Garbiyyah, inda ya tashi a cikin iyalai masu karatun kur’ani.

Ya hardace kur’ani mai tsarki tun ytana karami, haka nan kuma tn yana da shekaru 16 ya fara halartar wuraren karatun mai tsarki.

Yana da shekaru 24 ya fara gudanar da karatun kur’ani mai tsarki a gidan talabijin da radio na gwamnatin kasar Masar, kuma tun alokacin yana karatun ne da irin salon da aka san shi da shi a duniya.

Ya halarci taruka da dama a duniya karatun kur’ani, da hakan ya hada da kasashen Amurka, Birtaniya, Iran, Faransa da kuma Canada.

3472936

captcha