IQNA

Sabon Salon Rubutun Kur’ani A Syria A Lokacin Tunawa Da Juyin Iran

20:18 - February 06, 2016
Lambar Labari: 3480114
Bangaren kasa da kasa, ana koyar da daliban makarantu sabon salon rubutun kur’ani mai tsarki a wasu makarantu da Iran take daukar nauyinsu a Syria adaidai lokacin tunaw ada juyin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na smislo.com cewa, koyar da daliban makarantu sabon salon rubutun kur’ani mai tsarki a Syria da Lebanon da Jordan ana yinsa bisa mahangar jagoran juyin jya hali.

Kimanin dalibai 604 a makarantun kur’ania  cikin kasashen Syria, Lebanon, Palastinu da Iran suke koyon wannan salon rubutun kur’ani mai tsarki, bisa yanayi na rubutun kur’ani mai tsarki da aka fi sabawa da shin a Usman Taha.

Wasu daga cikin daliban da suka kamala wannan aiki sun aike da kwafin kur’ani mai tsarki da suka rubuta da hannu da wannan salon a rubutu ga ofishin jagoran juyin juyin juya halin muslunci.

A ranar tunawa da juyin juya halin mulunci ake sa ran za a mika wannn kwafi ga ofishin domik ashi ga jagora Ayatollah Sayyid Ali Khamenei (DZ)

Wadanda suka yi wanann kokari ne yara da makarantu da ke karkashin kulawar karamin ofishin jakadancin Iran a Syria, da ke Damscus, kamar yadda wasu kuma da suke kasar Lebanon da suka hada da palastinawa suka shiga cikin shirin.

Kasashen Syria da kuma Lebanon na daga cikin kasashen ma’aikatar kula da harkokin ilimi ta jamhuriyar muslunci ke bayar da muhimamnci a cikin wajen koyar da kananan yara ilmomin addini musaman ma dai karatun kur’ani mai tsarki.

3473269

captcha