
Kamfanin
dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar
gizo na smislo.com cewa, koyar da daliban makarantu sabon salon rubutun kur’ani
mai tsarki a Syria da Lebanon da Jordan ana yinsa bisa mahangar jagoran juyin
jya hali.
Kimanin
dalibai 604 a makarantun kur’ania cikin
kasashen Syria, Lebanon, Palastinu da Iran suke koyon wannan salon rubutun
kur’ani mai tsarki, bisa yanayi na rubutun kur’ani mai tsarki da aka fi sabawa
da shin a Usman Taha.
Wasu
daga cikin daliban da suka kamala wannan aiki sun aike da kwafin kur’ani mai
tsarki da suka rubuta da hannu da wannan salon a rubutu ga ofishin jagoran
juyin juyin juya halin muslunci.
A
ranar tunawa da juyin juya halin mulunci ake sa ran za a mika wannn kwafi ga
ofishin domik ashi ga jagora Ayatollah Sayyid Ali Khamenei (DZ)
Wadanda
suka yi wanann kokari ne yara da makarantu da ke karkashin kulawar karamin
ofishin jakadancin Iran a Syria, da ke Damscus, kamar yadda wasu kuma da suke
kasar Lebanon da suka hada da palastinawa suka shiga cikin shirin.
Kasashen
Syria da kuma Lebanon na daga cikin kasashen ma’aikatar kula da harkokin ilimi
ta jamhuriyar muslunci ke bayar da muhimamnci a cikin wajen koyar da kananan
yara ilmomin addini musaman ma dai karatun kur’ani mai tsarki.